10 Satumba 2020 - 09:56
Zarif: Iran Ba Za Ta Amince Da Dagewar Amurka Na Rabata Da Makamashin Nukliya Ba

Ministan harkokin wajen Iran Mohammad Jawad Zarif ya bayyana cewa, dagewar gwamnatin Amurka kan cewa Iran ba ta da hurumin amfani da fasahar makamashin nukliya ta zamanbinm sannan ba ta da hurumin seyan makamai don kare kanta da kuma ka da ta gina makamai masu linzami don kare kanta daga makiyanta ba amin amincewa ba ne ga mai hankali.

ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran Iran Press ya nakalto Zarif ya na fadar haka a cikin shafinsa na twitter a safiyar yau Alhamis.

Ya kuma kara da cewa shugaban Amurka Donal Trump ya bayyana haka ne ga wani dan jarida mai suna Bob Woodward, ya kuma kara da cewa Trump ya ce masa ya kera wani sabon makamin nukliya wanda babu wanda yake da irinsa a duniya.

A makon mai zuwa ne ake saran Bob Woodward zai kaddamar da wani littafi wanda ya rubuta, wanda kuma ya hada da hirar da ya yi da shugaban na Amurka kan wannan sabon makamin, wanda ya kira shi na asiri, amma kuma ya fadawa dan jarida.

342/